An fara zaɓen shugaban ƙasa a Malawi | Labarai | DW | 20.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara zaɓen shugaban ƙasa a Malawi

Da safiyar yau ne aka buɗe rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar Malawi, inda al'ummar ƙasar za su zaɓi sabon shugaba da 'yan majalisun dokoki gami da shugabannin ƙananan hukumomi.

Mutane miliyan bakwai da rabi da suka cancanci zaɓen ne za su kaɗa kuri'unsu, kuma ana ganin takara za ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci Joyce Banda da kuma Peter Mutharika wanda ƙane ne ga tsohon shugaban ƙasar da Joce Banda ɗin ta gada wato maragayi Bingu wa Mutharika. Hukumar zaɓen kasar ta ce za ta yi amfani da tsarin nan na dan takarar da ya fi yawan kuri'u wajen bayyana wanda ya yi nasara maimakon amfani da tsarin nan na kashi-kashi wanda aka saba gani a wasu kasashen nahiyar Afirka.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka haɗa zabukan shugaban ƙasa da na ƙananan hukumomi da na 'yan majalisun dokoki tun bayan da aka bijiro da wannan shirin a ƙasar sama da shekaru 20 din da suka gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane