An fara yaƙin neman zaɓe a Italiya | Siyasa | DW | 24.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An fara yaƙin neman zaɓe a Italiya

Tsofan shugaban gwamnatin Italiya Mario Monti ba zai yi takara ba a zaɓen 'yan Majalisar Dokoki

Ranar Asabar da ta wuce, shugaban ƙasar Italiya Giorgio Napolitano ya rusa majalisar dokokin, bayan murubus ɗin Firaminista Mario Monti, sanna shugaban ya ɗauki wani saban ƙuduri wanda ya ƙayyaɗe ranekun 24 da 25 gga watan Faburairu na shekara mai kamawa a matsayin ranar zaɓen 'yan majalisa.

A bayanin da yayi tare da manema labarai,Firaministan Italiya mai murabus Mario Monti, ya ce ba zai shiga takara ba, to amma a shirye ya ke, ya ɗauki muƙamin shugaban gwamnati idan buƙatar hakan ta taso.

Italian caretaker Prime Minister Mario Monti gestures during an end of the year news conference in Rome December 23, 2012. Monti said on Sunday that he would be ready to offer his leadership to political forces that adopt his agenda of reforms the country needs. REUTERS/Alessandro Bianchi (ITALY - Tags: POLITICS ELECTIONS)

Mario Monti

Yace:A shirye ni ke in bada gudummuwa ga aiyukan ƙasa.Idan wata jam'iya ko gungun jam'iyu suka buƙaci in ɗauki shugabacin gwamnati muddun suka kasance suna goyan bayan fasalin aiki da na ƙaddamar babu matsala, za mu iya haɗa kai mu yi aiki tare.

'Yan siyasa da dama sun yaba da ƙoƙarin Mario Monti, na tada komaɗar tattalin arzikin ƙasar, cikin tsukin watani 13 na jagoranci, saboda haka su ke tunanin sake ɗora masa yaunin cigaba da shugabanin gwamnatin Italiya, da zaran suka samu rinjaye a zaɓen da za a shiryawa ƙarshen watan Faburairu na shekara mai kamawa.

saidai tsofan Firaministan Italiya Silvio Berlusconi, ya yi wasti da cigaban da ake iƙirain Italiya ta samu a zamanin mulkin Monti:

Yace:Gwamnatin da aka kafa wadda ake wa kurari da gwamnatin ƙurraru ba ta tsinana komai ba, illa baƙar siyasar tsimi da tanadi, wadda sakamakonta ƙasa ta ƙara faɗawa cikin matsaloli.

Mario Monti ya yi bayani akan yadda jam'iyar Berlusconi ta kawo cikas ga yunƙurinsa na ceto Italiya daga halin talaucin da ta shiga, sannan ya bada shawarwari ga sabuwar gwamnatin da za ta hawa karagar mulkin ƙasar:

A view of the parlament while Italy's Prime Minister Mario Monti delivers an address on January 12, 2012 in Rome. Europe must make a greater effort to ensure growth, Italian Prime Minister Mario Monti said Thursday, hinting that the ECB should do more to help in the future once new budget rules are in place. AFP PHOTO / ANDREAS SOLARO (Photo credit should read ANDREAS SOLARO/AFP/Getty Images)

Majalisar Dokokin Italiya

Ya ce:Duk da ƙoƙarin da mu ka yi na tada komaɗar tattalin arziki, har yanzu akwai sauran rina kaba.Ba mu magance matsalar kwata-kwata ba.Amma na yi imanin cewar, Italiya na iya zama tarmamuwa a ƙasashen Turai, saidai kaimin mu cimma wannan matsayi, ya zama wajibi mu ƙara azama ta fannin ƙirƙiro husa'o'in cigaba, ta yadda nan gaba,za mu daina yin dogaro da tallafi daga kafofofin kuɗi na Asusun Bada Lamuni na Duniya kokuma na ƙasashen Turai.

Fasalin shugabaci da ya Mario Monti ya baiyana a jiya mai suna, cenza Italiya da yin kwaskwarima ga ƙungiyar Tarayya Turai ya ƙunshi matakai da dama na tsimi da tanadi domin bunƙasar tattalin arziki.

A cikin tsarin, Monti ya gabatar da hanyoyin yaƙi da zaman kashe wando, da kuma cin hanci da rashawa wanda suka yi ƙasar Italiya kanta.A ɗaya hannun, ya baiyana kyakkyawan fasali game da aiwatar da adalici a cikin al'amuran shari'a, wanda ya ce shine tushen kwanciyar hankali cikin ƙasa.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin