An fara tuhumar Shugaban hukumar Kwallon kafar Duniya a Switzerland | Labarai | DW | 25.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara tuhumar Shugaban hukumar Kwallon kafar Duniya a Switzerland

Tun a watan Mayun shekara ta 2015 hukumar Fifa ke bayar da hadin kai ga ofishin babban alkalin birnin Zurich tare da tattara muhimman bayanai daga hukumar.

FIFA Sepp Blatter mit Walter De Gregorio

Sepp Blatter

A yau ne a birin Zurich na kasar Switzerland aka fara tuhumar Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya wato Sepp Blatter abisa zarge-zargen cinhanci da karbar rashawa a hukumar gudanarwar kwalon kafar duniya.

Tun dai a ranar 27 ga watan mayun shekara ta 2015 hukumar FIFA ke bayar da hadin kai ga ofishin babban alkalin birnin Zurich tare da tattara muhimman bayanai ga ofishin.

A yayin da ofishin babban Antoney Janar yake fadawa manema rabarai a Zurich ya nunar da cewar an gudanar da bincike a ofishin shugaban hukumar kwallon kafar duniyar tare da yin awan gaba da muhimman takardu da ke da alaka da almundahanar kudaden hukumar.