1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara tattaunawa tsakanin Amirka da China

May 24, 2010

A lokacin wannan ziyara, Hillary Clinton ta isa Beijing da tawagar 'yan kasuwa da jami'an gwamnati kimanin 200.

https://p.dw.com/p/NVmO
Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Rodham ClintonHoto: AP

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta isa China domin tattauna hanyoyin cigaban kasuwanci da kuma magance matsalar tattalin arziki dake addabar duniya.

A jawabin sa wajen wani taro na haɗin guiwa Firaminista Hu Jintao yayi alƙawarin gudanar da sauye-sauye dake daya shafi darajar kuɗin ƙasar na Yean, amma kuma a bisa tsarin da ƙasar ta Sin zata amince dashi. A lokacin wannan ziyara, Hillary Clinton ta isa Beijing da tawagar 'yan kasuwa da jami'an gwamnati kimanin 200.

Clinton tayi amfani da ziyarar ta wajen taɓo matsalar nitsar da jirgin ruwan Koriya ta Kudu da ake zargin Koriya ta Arewa da aikatawa: tace yau muna fuskantar wani gagarumar kalubale daya biyo bayan nitsar da jirgin ruwan koriya ta kudu saboda haka akwai buƙatar aiki tare domin fuskantar ƙalubalen dake gaban mu na tabbatar da zaman lafiya a yankin tsibirin ƙasashen Koriya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi