An fara taron sauyin yanayi a birnin Bonn | Labarai | DW | 16.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara taron sauyin yanayi a birnin Bonn

Bayan watanni biyar da shimfida shirin yarjejeniyar sauyin yanayi a birnin Paris, jami'an diplomasiya sun fara wani taro karo na biyu domin duba yiwuwar fara aiwatar da ita.

Shugabar hukumar sauyin yanayin ta Majalisar Dinkin Duniya Cristiana Figueres ta fadawa mahalarta taron cewar.

Tabbas yanzu haka mun fahimci cewar akwai barazana a wannan shekarar da kuma yanayin yau da muke ciki,kuma muna cigaba da samun tarin bayanai daga gangaren kimiyya akan yadda yanayi ke kara yin sama ta yadda hakan ke shafar yanyin Duniya.

Kazalika ta kara da cewar duniya a dunkule take wajen ganin ta cimma duk wasu kudirorin da aka cimma a birnin Paris tare da shata tasawirar yadda za a kai ga dutun mun tsira.

To sai dai mahalarta taron da suka futo daga kasashe 196 sun bayyana cewar akwai gagarumin aiki agaba wajen kawar hayakin Carbon daga duniya nan da shekara ta 2020.