An fara taron NATO | Labarai | DW | 04.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara taron NATO

Shugabannin kungiyar tsaro ta NATO sun fara taro a Birtaniya kan manufofin gaba na kungiyar

Shugabannin kungiyar tsaro ta NATO/OTAN suna gudanar da taro a yankin Wales na kasar Birtaniya, inda suke neman hanyoyin katse kungoyiyn masu matsanancin ra'ayi na yankin Gabas ta Tsakiya, tare da duba halin da ake ciki a yankin gabashin kasar Ukraine.

Kungiyar tsaron ta NATO/OTAN za kuma ta duba makomar kasar Afghanistan bayan janyewar dakarun kasashen duniya a karshen wannan shekara ta 2014. Shugaban Amirka Barack Obama da Firaministan Birtaniya David Cameron sun ce babu gudu babu ja-da-baya wajen kawar da masu kaifin kishin Islama da suka kafa dauka wadanda suka hallaka Amirkawa biyu 'yan jarida. Akwai shugabannin kasashe kungiyar 28 da ke halartar taron.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu