1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara taron G20 cikin tsauraran matakan tsaro

Abdourahamane Hassane
July 7, 2017

Shugabannin kasashen G20 masu kafin masana'antu sun fara taronsu a birnin Hamburg na nan Jamus. An dai fara taron ne cikin tsauraran amtakan tsaro saboda jerin zanga-zanga da aka rika yi tun daga jiya Alhamis.

https://p.dw.com/p/2g8z0
Deutschland G20 Gipfel Familienfoto
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Yayin taron dai, shugabannin wannan kungiya ta G20 za su tattauna kan batutuwa da dama ciki kuwa har da halin da ake ciki a Siriya da kuma yunkurin da shugabannin za su yi waje shawo kan shugaban Amirka Donald Trump kan ya sauya matsayinsa dangane da ficewar da ya yi daga yarjejeniyar Paris din nan ta rage dudumamar yanayi a duniya.

A halin da ake ciki kuma yan sanda sun bukaci da aka kara aiko musu da karin karfi domin tinkara masu fafutuka da ke yin zanga-zangar adawa da taron tun a farkon wannan mako, wadanda aka shirya za su sake yin wani gangamin a yau. Gangamin na jiya da ya jawo tashin-tashina inda aka raunata mutane kana aka kama wasu daga cikin wanda ke zanga-zanga.