An fara shari′ar maharan Spain | Labarai | DW | 22.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara shari'ar maharan Spain

A wannan rana ta Talata ce mutane hudu da aka tsare ana zargi da hannu a harin Catalonia za su bayyana gaban kuliya don fiskantar shari'ar laifukan da suka aikata.

An dai tsara mutanen hudu da ke raye cikin wadanda ake zargi za su bayyana a gaban kuliya, abin da ke zuwa bayan halaka wasu mayakan da ke ikirari na Jihadi su takwas.

A ranar Litinin jami'an 'yan sanda a Spain sun bayyana cewa an harbe babban jigo a harin Barcelona Younes Abouyaaqoub, bayan dauki ba dadi da aka yi da shi, abin da ya kawo karshen nemansa ruwa a jallo da ake yi.

Shi dai Abouyaaqoub ya kasance cikin mutane 12 da ake zargi da kitsa amfani da mota wajen afkawa jam'a a Barcelona a wurin shakatawa na bakin ruwa a Cambrils, harin da kungiyar IS ta yi ikirari cewa ita ke da hannu a kai shi, karon farko a Spain.