An fara shari′ar janarorin Israila a Turkiya | Siyasa | DW | 06.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An fara shari'ar janarorin Israila a Turkiya

Ranar Talata kotu Turkiya ta fara tuhumar hafsoshin Israila da laifin kisan yan kasar magoya bayan Palesdinawa.

Ranar Talata a birnin Istanbul, aka fara shari'ar wasu janar-janar shida na Israila wadanda Turkiya take zarginsu da laifin kashe wasu yan kasar magoya bayan Palesdinawa. A wannan shari'a da ake ta muhawara kanta, jami'an sojan na Israila ana tuhumarsu ne da laifin kashe yan Turkiya dake cikin wani jirgin ruwa dauke da kayan agaji kan hanyarsa zuwa yankin Gaza a shekara ta 2010. Sharia'ar, wanda har ma zata shafi tsohon hafsan hafsosin Israila, ana yinta ne ko da shike wadanda ake tuhuma basu baiyana a gaban kotu ba.

Babban lauyan gwamnatin Turkiya tuni ya nemi yanke hukuncin daurin rai da rai har sau tara kan ko wanne daga cikin janarorin na Israila da ake tuhuma, saboda laifin kashe farar hula yan Turkiya dake cikin jirgin ruwan dauke da kayan agaji kan hanyar sa ta zuwa yankunan Palesdinawa. Israila a daya hannun, tun kafin a fara shari'ar ta kwatanta shi a matsayin al'amarin da Turkiya zata yi shi kawai domin cimma burinta ita kadai, saboda haka mahukunta a birnin Kudus suka ki baiwa takwarorinsu na Turkiya hadinkai. Haka nan kuma, kwararrun masu yawa na Israila suna shakkar ko wani kotu a Turkiya yana da hakki bisa shari'a ya tuhumci wadannan mutane, ko ya saurarri kararrakin dake kansu.

Aktivisten der Hilfsflotte in Gaza

Yan kare hakkin yan Adam cikin jirgin ruwan Mavi Maramara

Shekaru biyu da suka wuce, wasu masu akidar kare hakkin yan Adam daga kasashe 37 suka yi kokari cikin wani jirgin ruwa mai suna Mavi Maramara dauke da kayan agaji, su keta takunkumin da Israila ta kafa da ya toshe yankin Gaza gaba daya, domin isar da taimako ga Palesdinawa. Lokacin harin da sojojin Israila suka kaiwa jirgin ruwan yan Turkiya tara suka mutu, wasu 30 kuma suka sami rauni, inda a bisa maida martani, gwamnati a birnin Ankara kori jakadan Israila daga Turkiya. Gulden Sonmez, lauya, kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar agaji ta Islama mai suna IHH take cewa:

"Burinmu shine a hukunta Israila saboda wannan aika-aika da tayi. Sakamakon yarjejeniyar dake tsakaninmu ta mikawa juna masu laifi, muna fatan yan Israilan da muke tuhuma za'a kama su a wata kasar dabam, ko kuma hukumar yan sandan duniya ta Interpol ta bada gudummuwa a matakin kama wadannan mutane."

Guldern Sonmez tace muna sa ran za'a gudanar da shari'ar da zata zama ta tarihi, domin kuwa idan har aka sami janarorin na Israila da laifi, ana iya kama su a duk inda suka shiga a wannan duniya, ta hanyar amfani da hukumar yan sanda ta Interpol.

Mavi Marmara Gaza Flotte Jahrestag Istanbul

Masu zanga-zangar kyamar Israila a Istanbul

Tun da farko sai da gwamnati a birnin Ankara ta nemi Israila ta roki Turkiya gafara saboda kashe 'ya'yanta da tayi, ta kuma nemi Israilan ta biya iyalan wadanda aka kashe diyya, sa'annan ta sassauta toshewar da tayi wa yankin Gaza. Ministan Turkiya mai kula da dangantaka da kungiyar hadin kan Turai yace idan har Turkiya tana son kyautata dangantaka da kasar da tafi muhimmanci gareta a duniyar Larabawa, to kuwa tilas ne ta cika wadannan sharudda uku.

Kasashen biyu sun yi fiye da shekaru 50 da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu. Turkiya ita ce kasa ta farko ta musulmi da ta amince da wanzuwar kasar Israila, ta kuma bude ofishin jakadancin ta a kasar. Sai dai wani jami'in diplomasiya na Israila da bai so a ambaci sunansa ba, yace:

"Muna da ra'ayin cewar gwamnatin Turkiya ta Pirayim minista Recep Tayyip Erdogan tayi watsi da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin ta da Israila, a kokarin ta na samun karin angizo da fadi aji tsakanin kasashen duniyar Larabawa. To amma a yanzu, yana da muhimmanci ga kasashen biyu su dauki matakin kyautata fahimta tsakaninsu. Sabon kalubalken da ake fuskanta a wannan yanki ya sanya yin hakan ya zama wajibi."

A daura da haka, yan diplomasiya na Turkiya suna ganin halin da Israila take ciki a manufofinta na cikin gida ne ya haddasa lalacewar dangantaka tsakanin ta da Turkiya. A birnin Ankara yanzu dai ana jiran sakamakon zaben da za'a gudanar ne cikin watan Janairu a Israila. Yan diplomasiya suna fatan sakamakon zaben zai taimaka ga samun kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Yahouza Sadissou

Sauti da bidiyo akan labarin