An fara shari′ar al-Bashir | Labarai | DW | 19.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara shari'ar al-Bashir

Tsohon shugaban kasar Sudan Omar al Bashir ya gurfana a gaban kotu a Khartoum a wannan Litinin, domin fuskantar shari’a bisa tuhumarsa da aikata cin hanci da rashawa.

Sanye da fararen kaya irin na gargajiya, zaune cikin wani akurki na karfe da ke cikin kotun ta birnin Khartum,  magoya bayan tsohon shugaban sun barke da kabbara a yayin da hukumar yan sanda ta bayyana cewa ya karbi kudi kudi daga kasar Saudiyya.

Masu bincike a kasar ta Sudan na zargin shugaba el-Bashir da karbar kudi da suka kai dalar Amirka miliyan 90 daga yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed ben Salmane

Omar el-Bashir wanda ke tsare a wani gidan yari da ke birnin Khartum, hukumar mulkin sojan kasar na zarginsa ne da tara makudan kudade fiye da dalar Amirka miliyan dari da 13 a yayin wani samame da suka kaddamar a gidansa, jim kadan bayan hambarar da shi daga madafan iko.