1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara samun sakamako a zaben Tunisiya

Suleiman Babayo
September 16, 2019

Sakamakon farko na zaben Tunisiya ya nuna cewa yuwuwar za a tafi zagaye na biyu tsakanin Farfesa masanin sharia Kais Saied da mai mallakan kamfanonin sadarwa Nabil Karoui.

https://p.dw.com/p/3PfmT
Präsidentschaftswahl in Tunesien 2019 | Stimmauszählung in Tunis
Hoto: Reuters/M. Hamed

Sakamakon farko na zaben Tunisiya ya nuna cewa dole za a tafi zagaye na biyu. Sakamakon ya nuna Farfesa masanin sharia Kais Saied da mai mallakan kamfanonin sadarwa Nabil Karoui ke kan gaba bayan kirga kashi 27 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben na wannan Lahadi da ta gabata.

Kais Saied dan shekaru 61 da haihuwa yana da kashi 19 cikin 100 yayin da Nabil Karoui dan shekaru 56 ke da kashi 14 da doriya cikin 100. Dan takarar jam'iyyar mai ra'ayin addinin Islama ta Ennahdha, Abdelfattah Mourou ke matsayi na uku da kashi 13 cikin 100.

Kimanin kashi 45 cikin 100 na masu zabe suka kada kuri'a a zaben na biyu tun da kasar ta koma tafarkin dimukuradiyya a shekara ta 2011 bayan juyin juya hali. Idan babu dan takara da ya samun adadin da ya haura kashi 50 cikin 100 za a tafi tagaye na biyu na zabe a kasar ta Tunisiya da ke yankin arewacin nahiyar Afirka.