An fara samun galaba kan ′yan IS a Iraki | Labarai | DW | 17.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara samun galaba kan 'yan IS a Iraki

Dakarun Kurdawa a Iraki sun ce sun fara samun galaba a kokarin da suke yi na karbe iko da yankunan da masu kaifin kishin addini suka kwace a Mosul.

Wata majiya daga yankin ta ce sojin na Kurdawa tare da tallafin sojin Amirka sun karbe iko da kauyukan Telsqod da Risala wadandan ke da tazarar kilomita 30 arewa da birnin na Mosul.

Majiyar har wa yau ta ce sojin na kokarin dannan kai yanzu haka zuwa yankunan da ke kusa da dam din Mosul wadanda suka fada hannun 'yan IS don karbe iko da su.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da sojin Amirka suka kai farmaki ta sama har sau tara kan mayakan IS din daura da dam din na Mosul da kuma garin na Irbil da ke yankin na Kurdawa, inda rahotanni ke cewar hare-haren sun lalata makaman 'yan fafutukar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu