An fara mayar da mayakan IS kasashensu | Labarai | DW | 11.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara mayar da mayakan IS kasashensu

Gwamnatin Turkiyya ta tisa keyar wasu tsoffin mayakan IS biyu zuwa kasashensu na asali a kokarin da take na ganin an raba mayakan da kasar Siriya a yayin da take ci gaba da fada da mayakan Kurdawa.

A makon da ya gabata ne dai, gwamnatin Ankarar ta yi shelar soma aikin mayar da mayakan da ake tsaresu dasu a gidajen yarin Siriya. Akwai wasu saura ashirin da uku da suka fito daga kasashen yankin Turai da tace za ta mayar a 'yan kwanaki masu zuwa.

A watan da ya gabata ne dai, rundunar sojojin kasar Turkiyya ta kaddamar da farmaki a yankin arewacin kasar Siriya don fatattakar mayakan Kurdawa. Kasashen duniya sun nuna adawa da farmakin inda suka baiyana damuwa kan makomar mayakan na IS da ake tsare da su a gidajen yari, amma kuma sun yi biris da kiran gwamnatin Ankaran kan kwashe tsoffin mayakan zuwa kasashensu na asali.

Rahotannin sun tabbatar da cewa, an sami 'yan IS da dama da suka kubuta a sakamakon fadan. Galibinsu wadanda suka bar kasashen Turai suka tafi Siriya ne da sunan jihadi da kuma rundunar kawance ta yi nasarar kamawa.