1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kirga kuri'a a zaben kasar Burundi

Suleiman BabayoJuly 22, 2015

Shugaba Nkurunziza na Burundi ya kama hanyar sake lasjhe zabe a karo na uku mai cike da rudani da 'yan adawa suka kaurace.

https://p.dw.com/p/1G3M6
Burundi, Wahllokal in Bujumbura
Hoto: DW/K. Tiassou

Kwana daya bayan zaben shugaban kasar Burundi mai cike da rudani, an fara kirga kuri'u a wannan Laraba. Ana sa ran Shugaba Pierre Nkurunziza zai sake samu wa'adi na uku a zaben da ya gamu da tashe-tashen hankula gami da tofin tir daga kasashen duniya.

Shugaban hukumar zabe ya ce kashi 74 cikin 100 na masu zabe milyan uku da dubu-800 suka kada kuri'a a zaben da manyan jam'iyyun adawa suka kaurace saboda tazarce da ya saba ka'ida da Shugaba Nkurunziza dan shekaru 51 yake nema, abin da ke neman sake jefa kasar cikin yakin basasa. Kasar ta Burundi da ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Beljiyam a shekarar 1962 ta fuskanci tashe-tahse hankula masu nasaba da kabilanci.