An fara kaɗa ƙuri′a a Scotland | Labarai | DW | 18.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara kaɗa ƙuri'a a Scotland

Sama da mutane miliyan huɗu ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen raba gardama dangane da samun yanci cin gashin kai daga Burtaniya.

Tun da farko hasashen zaɓen da aka gudanar ya nuna cewar masu neman samun yancin kan sune za su samu nasara.sai dai Burtaniya ta ci gaba da yin fafutuka har a jiya a rana ta ƙarshe ta yaƙin neman zaɓen domin samun goyon bayan jama'a.

Gordon Brown tsohon firaministan Burtaniya ya gargaɗi al'ummar ta Scotland da ta yi dogon nazari wajen yanke shawarar da ta dace, domin ka da su yi, nadama daga baya.Wannan zaɓe dai duniya ta zura ido ta ga yadda zai kaya.