An fara isa inda guguwa ta yi ɓarna | Siyasa | DW | 15.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An fara isa inda guguwa ta yi ɓarna

Masu aikin ceto sun fara isa yankunan da mahaukaciyar guguwa ta yi wa illoli inda yanzu mazauna yankin su ka fara gyara gidajensu

Tsibirin Leyte da ke ƙasar Philippines na ɗaya daga cikin waɗanda mahaukaciyar guguwar Taifun Haiyan ta aukawa. Kimanin mako guda da faruwar lamarin, amma har yanzu akwai dubban mutane da ke zaune a tsibirin ba tare da wutar lantarki ko ruwan sha mai tsabta, haka kuma rufin ɗakunan duk sun ɗaye. Amma duk da haka tsibirin ɗaya ne daga cikin tsibiran da guguwar ta shafa, da ake da kekkewar fata.

Die Insel Leyte wurde besonders schwer getroffen vom Taifun Haiyan. Fast eine Woche nach dem Sturm sind dort noch immer tausende Menschen ohne Strom und Trinkwasser. An einigen Orten gibt es jedoch Hoffnungszeichen. Regen unterbricht in Merida immer wieder die Aufräumarbeiten. Foto: Peter Hille DW 14.11.2013

Tsibirin Leyte

"Wannan dai wani mazaunin tsibirin ne ke faman sake rufe ɗakinsa. Ɗaukacin babban titin dai ya cika da tarkace, ko da yake wasu fallen kwanon ana iya sake yin amfani da su, inda ake saran sakewa mutane dubu ɗaya rufin kwanonsu.

Waɗanda suka rasa dangi

Yayinda wasu ke fafitikar gyara gidajensu. Shi kuwa Roberto Rome ya zauna a gabar ruwa ya na kallon kasa inda ya ke tunawa da matarsa, wanda mahaukaciyar guguwar ta yi awun gaba da ita.

"Wata biciya ce ta faɗo a kanta. kuma shi ne ya kasance ajalinta"

Yayinda wasu suka yi kokarin gudu lokacin guguwar har suka tsira, amma wasu sun tsira da raunuka, inda a yanzu su ke jinya.

Survivors stay inside a battered house damaged by super typhoon Haiyan in Tanauan, Leyte in central Philippines November 14, 2013. Philippine President Benigno Aquino was under growing pressure on Thursday to speed up the distribution of food, water and medicine to desperate survivors of a powerful typhoon and to revive paralysed local governments. REUTERS/Erik De Castro (PHILIPPINES - Tags: DISASTER ENVIRONMENT)

Barnar guguwa a Philippinen

A yankin dai har yanzu anan kwarar ruwan sama. Mutanen wannan tsibirin, a yanzu haka kowa ya makale a ɗaki. A karkashin ɗakunansu waɗanda aka sake ginawa bayan guguwar. Kuma kawo yanzu babu wani tallafi da ga waje da ya iso yankin.

Sandara Bulling da ke wata kungiyar bada tallafi ta International Care, ta bi gabar tekun na tsawon kilo mita 30, ta na ɗaukar hotunan yankin, kuma ta sadu da matasa da dama wadanda ke matukar bukatar abinci.

"A yanzu haka kayan abinci da mu ke son kawo nan domin tallafawa mutanen ya na kan hanya dagabirnin Manila, Kuma da zaran ya iso nan ta ke za mu fara rarrabawa jama'a. Kamar a cikin tsarin shi ne, irin wannan yankunan da matsalar ta shafa, mu na saran za mu iso su. Ka zalika muna saran kawo kayan gini a wannan yankin, don taimakawa mutanen su sake gina gidajensu.

Tallafi ya fara isa wasu ƙauyuka.

Die Insel Leyte wurde besonders schwer getroffen vom Taifun Haiyan. Fast eine Woche nach dem Sturm sind dort noch immer tausende Menschen ohne Strom und Trinkwasser. An einigen Orten gibt es jedoch Hoffnungszeichen. Im Rathaus von Ormoc kommt Hilfe an. Foto: Peter Hille DW 14.11.2013

Kayan agaji

Wannan dai hayaniya ce ta kayan da ya iso wani kauyen da ake kira Ormoc. Nan da nan masu aikin sa kai su ka fara saɓan buhunan shinkafa da ruwan sha, don rarabawa muta ne. Ko da ofishin karamar hukumar da aka ajiye kayan ma, shi ma rufin kwanonsa wasu bangaren sun ɗaye. Don haka jami'an tsaro na sintiri don samar da tsaro. Bingo Capahi shi ne kakakin karamar hukumar ta Ormoc.

"Ormoc ta shafu matuka. Babban abinda mutanen ke buƙata cikin gaggawa shi ne kayan tallafi. Lamarin yana da wuya, amma dai muna kai. Domin kuwa tashar jiragen sama da ta ruwa, ba su lalace sosai ba. Don haka suka ce mana, Ormoc ce za ta kasance cibiyar da za a jibge kayan agaji, ga ɗaukacin yankin Leyte, don haka muna iya kokarinmu"

Idan rana ta faɗi babu abinda mutun ya ke ganin a Ormoc, illa tociloli da a ke haskawa, domin yankin ya kasance babu wutar lantarki.

A ƙasa kuna iya sauraron sautin rahoton da kuma Shirin Mutun da duniyarsa a kan guguwar da ta faru a Philippines

Mawallafa: Peter Hille / Usman Shehu Usman
Edita: Pinado Abdu

Sauti da bidiyo akan labarin