An fara gudanar da zabe a gabashin Ukraine | Labarai | DW | 02.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara gudanar da zabe a gabashin Ukraine

Duk da barazanar kasashen yamma da ma Ukraine ke yi na cewa ba za su aminta da wannan zabe ba, zaben ya soma a jihohin Donetsk da Lougansk.

Tun dai musalin karfe biyar agogon GMT ne, kofofin runfunan zaben suka buda inda kawo yanzu al'ummar yankin ke ci gaba da kada kuri'un su domin zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisu wanda ake ganin idan har hakan ya wakana, to wannan yanki zai kara yi wa hukumomin Ukraine nisa a kokarin da suke na karbar sa, tare da neman dunkule kasar wuri daya.

Zaben dai na gudana ne, yayin da aka sake komawa ga fada tsakanin dakarun 'yan awaren da na gwamnatin Ukraine, rikicin da kawo yanzu ya yi sanadiyar rasuwar mutane fiye da 300 a cikin kwanakin nan goma na baya-baya duk kuwa da batun tsagaita wutar da aka cimma.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo