An fara ganin lamar sasanta rikicin Yukurain | Labarai | DW | 28.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara ganin lamar sasanta rikicin Yukurain

'Yan majalisar dokokin ƙasar Yukrain sun kaɗa ƙuri'ar amincewa a soke dokar da ta haramta yin zanga-zanga

Wannan dokar haramta zanga-zanga dai ita ce ta ingiza 'yan adawa suka zafafa bore sama da makwanni hudu. Shugaba Viktor Yanukovych ya sanar da alamar cire dokar tun a jiya Litinin, bayan ganawarsa da shugabannin 'yan adawa. Ya kuma yi alƙawarin yi wa masu fafitika da aka tsare afuwa. To sai dai fa ministar shar'ar ƙasar tuni ta ce, duk wadannan matakan za a yi aiki da su ne kawai, idan masu boren suka bi wasu sharruɗa. Wato afuwar za ta fara aiki ne kawai idan wadanda suka mamaye gine-ginen gwamnati suka janye, kana aka baiwa tituna sarari don matafiya. Idan haka bai faru ba, to afuwar da aka sanar ba za ta fara aiki ba. babu dai tabbaci ko masu boren da ke neman shugaban ƙasa ya yi murabus, za su yi biyya ga wannan sharaɗin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu