An fara binciken Firaministan Isra′ila | Labarai | DW | 04.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara binciken Firaministan Isra'ila

Tsohon shugaban ma'aikata a fadar Firaministan Isra'ila Benjamin Natanyahu, ya sanya hannu kan wata takardar bada shaida kan kan wasu zarge-zargen rashawa da ke kan Firaministan.

Jaridun kasar Isra'ila sun ce tsohon shugaban ma'aiktan fardar Isra'ilar Ari Harow na iya samun sassauci a binciken da 'yan sanda ke yi a kansa shi ma. Ana dai zargin Firaministan na Isra'ila Natanyahu ne da karbar wasu kyautuka da ake ganin sun saba doka daga hannun wasu 'yan kasuwa da kuma nuna son zuciya da ya yi kan aikace-aikacen wasu kafofin labarai a Isra'ila.

Akwai ma batun shirye shirye da ya ke yi na sayen wasu manyan jiragen ruwan Jamus da suka kai na biliyoyin daloli, wanda nan ma ake bincikensa a kai.