1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN FARA BA DA KAIMI WAJEN ZABEN `YAN TAKARA A ZABEN SHUGABAN KASAR JAMUS

YAHAYA AHMEDMarch 3, 2004

A cikin wannan shekarar ne za a zabi sabon shugaban kasa a nan Jamus. Zaben, wanda za a yi a cikin watan Mayu mai zuwa, ya janyo wata muhawara a bainar jama'a kan `yan takarar da jam'iyyun adawa za su zaba su tsaya a zaben.

https://p.dw.com/p/BvlX
Shugabannin jam'iyyun adawa na CDU/CSU da FDP, a ganawar da suka yi a Berlin
Shugabannin jam'iyyun adawa na CDU/CSU da FDP, a ganawar da suka yi a BerlinHoto: AP

A duk shekaru biyar-biyar ne ake zaben shugaban kasa a nan Jamus. Amma wannan zaben ba na gama gari ba ne, kamar na shugaban gwamnati. Majalisun tarayya ne ke zaban shugaban kasar a madadin duk al’umman kasa baki daya. A halin yanzu dai, matsayin da ake ciki shi ne: jam’iyyar adawa ta CDU/CSU ba ta da rinjayi a majalisar dokoki. A majalisar mashawarta kuma, jam’iyyun gwamnati na SPD da Greens, su ma ba su da rinjayi. A yanzu dai jam’iyyar nan ta FDP ce ake sa wa ido. Saboda duk bangaren da ta goyi bayansa, shi zai iya tsai da dan takara a zaben, don kuma ya ci nasara.

A jiya talata ne dai, jam’iyyar CSU ta ba da sanarwar cewa, manyan jam’iyyun adawan biyu a majalisar dokoki sun amince da tura dan takara guda daya a zaben. Wannan kuwa, shi ne tsohon ministan harkokin cikin gida da kuma tsohon shugaban jam’iyyar CDU, Wolfgang Schäuble. Kai tsaye ne dai shugaban jam’iyyar ta CDU, Angela Merkel, ta karyata wannan sanarwar. Daga baya ne kuma shugabannin jam’iyyun CDUn da CSU da FDP, wato Angela Merkel, da Edmond Stiober, da Guido Westerwelle suka gana da juna don tsai da shawara kan wanda za su tura ya tsaya a zaben, amma ba su cim ma wani sakamako ba. Bisa dukkan alamu dai, Guido Westerwelle ya ki amincewa da zaban Wolfgang Schäuble tamakar dan takaran jam’iyyun adawan. Bayan wannan taron ne, Edmond Stoiber, shugaban jam‘iyyar CSU, kuma Firamiyan jihar Baveriya, ya bayyana cewa:-

"Har ila yau dai, ina kyautata zaton cewa za mu cim ma nasarar fid da dan tankara guda daya, wanda jam’iyyun na CDU/CSU da kuma FDP za su amince da shi. Idan ko ba a cim ma daidaito ba, sai mu ci gaba da tattaunawa."

Da farko dai, shugabannin jam’iyyun ne za su yi shawarwari tsakaninsu, kafin su tsai da wata shawara. Amma kafin hakan ma, ana yada rade-radin cewa, mai yiwuwa a kauce daga zaban Schäublen. Wasu na ganin cewa, ministan al’adu ta jihar Baden-Württemberg, Annette Schavan ce za ta sami amincewar duk bangarorin jam'iyyun adawan.A cikin wata fira da ya yi da gidan talabijin nan ZDF na nan Jamus, mataimakin shugaba jam’iyyar FDP Andreas Pinkwart ya bayyana cewa:-

"Abin da muke tattaunawa da Merkel da Stoiber a halin yanzu, shi ne mu ga yadda za mu sami hadin kai, tare da yunkurin da jam’iyyar FDP ke yi, wajen magance matsalar. Ina kuma ganin yiwuwar wannan yunkurin namu."

Shi dai Pinkwart ya fi goyoyn bayan tura dan takara daga jam’iyyarsa ta FDP, wato Wolfgang Gerhardt, tsohon shugaban jam’iyyar ne zuwa zaben. Amma mafi yawan `yan jam’iyyar sun nuna ra’ayin bai wa `yar takara mace fiffiko da namiji. Saboda a nasu ganin, bayan shekaru 50 da kafa Jaumhuriyar Tarayyar Jamus, lokaci ya zo da ya kamata a ce an sami farkon shugaban kasa mace a tarihin wannan kasar.

Wasu majiyoyi na nuna cewa, jam’iyyun gwamnati na SPD da Greens ma na goyoyn bayan wannan ra’ayin. Bisa dukkan alamu dai, tsai da Wolfgang Schäuble tamkar dan takarar jam’iyyun adawan, ba zai sami amincewar jama’a ba.

Wani binciken da aka gudanar na nuna cewa, kashi 48 cikin dari na jama’ar da aka yi wa tambayoyi ne, suka nuna rashin goyon bayan tsai da Wolfgang Schäuble din tamkar dan takara.