An fara aikin Hajji a kasa mai tsarki | Labarai | DW | 08.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara aikin Hajji a kasa mai tsarki

An fara gudanar da aikin hajjin bana a kasa mai tsarki wato Saudiya. Musulmi kimanin miliyan 2.5 ne suka tashi yau daga birnin Makkah zuwa garin Mina, inda zasu kwana a karkashin tantunan da aka kakkafa kafin a yi hawan dutsin Arafat a gobe, lokacin da aikin hajjin na bana zai kai kololuwarsa. Hajji dai na daga cikin shika-shikai 5 na addinin musulunci. A wani kokari na tinkarar duk wata turereniya da ka iya aukuwa ko hare haren ta´addanci, a bana hukumomin Saudiya sun girke jami´an tsaro kimanin dubu 60 yayin da dubban ma´aikatan kiwon lafiya ke cikin shirin ko-takwana. A cikin makon jiya maniyata 76 suka rigamu gidan gaskiya sakamakon rushewar wani karamin otel a birnin Makkah.