An doshi hanyar kawo karshen cutar Polio | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 20.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

An doshi hanyar kawo karshen cutar Polio

Bisa ga dukkan alamu an kusan yin bankwana da cutar shan-inna a nahiyar Afirka bayan an tsawon lokaci ba a samun sabbin wadanda suka harbu da ita ba.

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a wannan makon ta mayar da hankali a kan cutar shan-inna ko Polio tana mai cewa bisa ga dukkan alamu an kusan yin bankwana da wannan cuta a nahiyar Afirka bayan da bayanai suka nuna cewa tarayyar Najeriya ta doshi hanyar samun galaba a kan cutar mai nakasa kananan yara.

Ta ce shin wa ya taba yin tunanin wannan? Najeriya da a shekarun bayan nan ta shiga kanun labarun duniya dangane da tashe-tashen hankula na masu ta da kayar baya musamman a yankin arewa maso gabashin kasar, yanzu tana kan kyakkyawan hanyar kawar da cutar shan-inna. Tun a watan Yulin bara ba a sake samun labarin sabbin wadanda suka kamu da cutar ba. A hukumance dai idan aka kwashe tsawon watanni hudu ba a samu wanda ya harbu da cutar ba, to kenan an shawo kanta. Jaridar ta ce wannan albishir ne a kasar ta Najeriya inda yakuwar kawar da cutar ta yi ta fuskantar adawa mai tsauri, inda a wasu lokuta aka yi ta kai hari tare da hallaka wasu jami'an kiwon lafiya masu yi wa yara riga kafin cutar.

Kokarin magance yunwa a Afirka

Savanne Kolumbien Akazienplantage

Yankin Savannah ka iya magance matsalar yunwa a Afirka

Ita ma jaridar Frankfurter Allgeimeine Zeitung a wannan makon labari mai dadin ji ta buga game da Afirka inda ta rawaito wata tawagar masu binciken kimiyya ta kasa da kasa na bayyana imanin cewa yankin Savannah da ke kudu da Sahara ya dace da zama wani yanki da zai magance matsalar yunwa a nahiyar. A dangane da yanayin yankin mai samun ruwan sama a kai a kai da kuma tarin albarkatun ruwa ga aikin gona , hukumar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma Bankin Duniya sun zabi yankin a matsayin wani wurin aikin gona na lokaci mai zuwa nan gaba. Rahoton hukumomin biyu ya ce ana iya yin noma a wani fili mai fadin hekta miliyan 400 wajen samar da hatsi da kuma tsirrai da za a iya amfani da su wajen samun makamashi.

Kame masu fafatukar girke demokradiyya

Joseph Kabila Kabange

Shugaba Joseph Kabila na Kwango

Har yanzu ana tsare da masu fafatuka inji jaridar Die Tageszeitung a labarin da ta buga game da halin da ake ciki a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango inda ta rawaito jaridun kasar masu goyon bayan gwamnati na kiran masu fafatukar demokradiyya daga kasashen Senegal da Burkina Faso 'yan ta'adda. Hukumomin Kwangon sun tsare masu fafatuka uku daga Senegal da daya daga Burkina Faso da kuma takwarorinsu da dama na kasar ta Kwango lokacin wani taro a karshen mako. An dai gayyacesu taron ne wanda a karshe aka shirya yin wani biki don kalubalantar take-taken shugaban Kwango Joseph Kabila na neman yin tazarce bayan cikar wa'adin mulkinsa a shekarar 2016.

Binciken ta'asa a Eritrea daga ketare

Kwararrun masana na Majalisar Dinkin Duniya na kokarin gudanar da bincike a kan cin zarafin jama'a, yunwa da talauci a kasar Eritrea ba tare da sun shiga kasar ba, domin an hana su izinin shiga kasar ta Eritrea inji jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ce a Eritrea dai kama mutane ana tsare su ya zama ruwan dare, kuma wannan ya fi shafan matasa maza da mata wani lokaci ma har da kananan yara. Hukumar kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wata hukuma don gano dalilan da ke angiza akasarin 'yan Eritrean yin kaura zuwa ketare.