An doke Moroko a karbar bakuncin kwallon kafa | Labarai | DW | 13.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An doke Moroko a karbar bakuncin kwallon kafa

Amirka da Mexico da kuma Kanada sun buge kasar Moroko inda kasashen da suka shigar da bukatar hadin gwiwar za su dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekarar 2026.

Hukumar FIFA ce ta sanar da hakan a wannan Laraba bayan da aka kada kuri'a kuma gamayar kasashen ukun suka sami yawan kuri'u dari da talatin da hudu da suka zarta Moroko mai kuri'u sittin da biyar, an kada kuri'a a birnin Moscow na kasar Rasha gabanin soma gasar 2018 da Rashan ke daukar nauyinta.

Wannan shi ne karo na biyar da kasar ta Moroko ke shan kaye bayan ta kai wannan mataki amman kuma ta gagara samun damar daukar nauyin gasar.