An dakile shirin ta′addanci a Ostareliya | Labarai | DW | 30.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dakile shirin ta'addanci a Ostareliya

Jami'an tsaro a Ostareliya sun sanar da yin nasarar bankado wani shiri na kai harin ta'addanci kan jiragen sama a kasar inda maharan ke son yin amfani da wata na'ura mai tarwatsewa da suka kirkira wajen kado jiragen.

Jami'an tsaron kasar Ostareliya sun sanar da yin nasarar bankado wani shirin kai harin ta'addanci kan jiragen sama a kasar inda maharan ke son yin amfani da wata na'ura mai tarwatsewa da suka kirkira wajen kado jiragen saman. Firaministan kasar Malcolm Turnbull ne ya sanar da hakan a wannan Lahadi a lokacin wani taron manema labarai inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

A yammacin jiya mun kaddamar da wani gagarumin bincike da ya bamu damar hana wani harin ta'addanci na kado jirgi da aka kitsa. Muna ci gaba da bincike kuma ya zuwa yanzu mun kama mutane hudu.

Mahukuntan kasar ta Ostareliya sun bayyana cewa ya zuwa yanzu ba su kai ga gano inda aka so kai harin da kuma ranar da aka so a kai shi ba, kana ba su yi bayani a kan ko maharan na da niyyar kai harin kan jirgin saman fasinjar kasa da kasa ne ko kuma na cikin gida ba.