1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ANC ta dakatar da sakatarenta

Suleiman Babayo
May 5, 2021

Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ta dakatar da sakataren jam'iyyar Ace Magashule har zuwa lokacin da za a samu sakamakon shari'ar da yake fuskanta kan cin hanci.

https://p.dw.com/p/3t0iU
 Ace Magashule I südafrikanischer Politiker I African National Congress
Hoto: Gianluigi Guercia/AFP/Getty Images

Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ta dakatar da sakataren jam'iyyar Ace Magashule har zuwa lokacin da za a samu sakamakon shari'ar da yake fuskanta kan cin hanci da rashawa nan gaba cikin wannan shekara.

Magashule mai shekaru 61 da haihuwa tun farko an ba shi wa'adin kwanaki 30 ranar 30 ga watan Maris domin ya ajiye mukamun saboda tuhuma kan almubazzaranci da duniyar gwamnatin lokacin da yake rike da mukamun pirimiya a lardin Free State. Tuni dai Ace Magashule ya musanta tuhumar da ake masa. Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu tun lokacin da aka koma tafarkin demokaradiyya da kowa ke iya zabe tana neman gyara sunanta da ya baci sakamakon zarge-zargen da ake yi wa jami'an na cin hanci da rashawa a shekarun da suka gabata.