An dakatar da jam′iyyun adawa don ingiza tarzoma | Labarai | DW | 08.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dakatar da jam'iyyun adawa don ingiza tarzoma

Gwamnati kasar Chadi ta sanar da dakatar da wasu jam'iyyun adawa guda 10 bisa zargi na abun da ta kira ingiza tarzoma a tsakanin al'umma.

Matakin gwamnati ya biyo bayan zanga zangar kungiyoyin kwadago da jami'yyun suka jagoranta dangane da matakin tsuke bakin aljihu na gwamnatin.

Acewar ministan tsaron Chadin Ahmat Mahamat Bachir, an dakatar da ayyukan jam'iyyun na tsawon watanni biyu, saboda abun da ya kira dalilai na tsaron kasa.

Daura da haka hukumomin kasar sun sanar da haramta jerin gwano da ake shirin yi akan tituna a wannan Alhamis a karkashin jagorancin kungiyoyi masu zaman kasansu da na kwadago da jam'iyyun adawa.