An dakatar da fidda sakamkon zaben Malawi | Labarai | DW | 26.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dakatar da fidda sakamkon zaben Malawi

Kotu a a kasar Malawi ta samu karaki har 147 daga jam'iyyun da suka shiga zaben da ya gudana a makon jiya, tuni dai bore ya barke daga bangaren 'yan adawa, masu boren sun yi ta yaga postocin jam'iyya mai mulki

Lazarus Chakwera, na Malawi Congress Party (MCP) ya fada wa kotun cewa sun gano kura-krai a gundumpomi 10 cikin gundumomi 28, inda aka yi aringizon kuri'u lokacin kada kuri'a, bisa yin amfani da tawada da kuma birkita takardun zabe. Don haka babban kotun kasar ya umarci a dakatar da bada sakamakon zaben, har sai an sake kirga wasu gundomomi da ake da shakku a kansu. Babbar daraktar hukumar zaben kasar Jane Ansah, ta bayyana cewa a yanzu ba za ta ci gaba da sanar da sakamako ba, har sai an kammala ka'idojin shari'a. A bisa dokokin kasar Malawi, duk wasu korofe-korofen zabe sai an kammala su, kana a sanar da sakamakon zaben a tsukin kwanaki takwas bayan zabe. Tuni dai bore ya barke daga bangaren 'yan adawa, inda a Lilongwe babban birnin kasar, masu boren suka yi ta yaga postocin jam'iyya mai mulki, kana suka yi ta fasa gine-ginen gwamnati. An dai baza jami'an 'yan sanda don shawo kan lamarin. Shugaba Peter Mutharika na neman wa'adi na biyu amma yana fiskantar mummunar adawa.