1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dage zaman shari'ar alkalin alkalan Najeriya

Uwais Abubakar Idris GAT
January 14, 2019

A Najeriya awoyi kalilan bayan soma zaman farko na shari'ar Alkalin Alkalai Walter Onnonghen da ake zargi da kin bayyana kadarorinsa, Kotun Da'ar Ma'aikata ta dage zaman shari'ar a bisa dalilai dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/3BWFQ
Walter Samuel Nkanu Onnoghen Chief Justiz für Nigeria
Hoto: Ubale Musa

Alkalin Alkalan Najeriya Walter Onnonghen ya ki bayyana a kotu a ranar farko ta fara shari’ar da gwamnatin Najeriya ta gabatar a gaban Kotun Da’ar Maikata bisa zargin kin bayyana kadarar da ya mallaka. Wannan dai shi ne karo na farko a Najeriya da ake zargin babban alkalin kasar.


Tun da safiyar ranar Litinin dai ‘yan sanda suka kewaye daukacin kotun ta da’ar ma’ikata abin da ya nuna girma da muhimmancin shari’ar wacce wasu masu fafutukar tabbatar da 'yanci da adalci suka fara zanga-zanga tun kafin ma a fara shari’ar a karkashin jagorancin Alkali Danladi Umar. To sai dai babban lauyan da ke jagorantar masu kare wanda ake tuhuma Barrister Wole Olanipekun ya fara da kalubalantar kotun kan cewa ba ta da hurumi na sauraren wannan shari’a, don haka babu batun ma wanda ake zargi ya bayyana a gabanta.

Nigeria Gerichtshof in Abuja
Hoto: DW/U. Musa


Lauyan gwamnati da ke jagorantar masu tuhuma, Aliyu Umar, ya ce dole ne wanda ake zargi ya fara bayyana kafin a yi batun hurumi ko akasin haka. To sai dai Barrsiter Olanipekun ya bullo da wata sabuwa cewa ai ba’a bai wa wanda ake tuhuma Walter Onnonghen sammaci ba, domin mai taimaka mashi ne ya amshi takardar sammacin kotu ba shi ba. An dai ta musayar dogon Turanci da kawo dalilai na tsarin mulki a kan wannan batu da a karshe kotu ta amince da a sake aikawa da sammaci ga wanda ake tuhuma kamar yadda doka ta ce. To sai dai lauyan da ke kare Walter Onnonghen, Barrsiter Wole Olanipekun ya ki cewa uffan a kan shari’a.


An sanar wa kotun cewa sama da lauyoyi 43 ne ke kare babban jojin Najeriyar a shari’ar da ta sanya mai da martnai da ma zargin akwai dalilai na siyasa a cikinta. Barrsiter Erasse Ejingbon na kungiyar lauyoyin Najeriya ya ce sun kai su 300 da suka zo kotu don kalubalantar zargin.

Walter Samuel Nkanu Onnoghen Chief Justiz für Nigeria
Hoto: Ubale Musa

Daga karshe dai an dage sauraren shari’ar har zuwa ranar 22 ga watan nan na Janeru. Masharhanta na bayyana mamakin yadda aka kawo karar a Kotun Da’ar Ma'aikata bayan kuwa ko da a lokacin da aka tuhumi Shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki batun rashin hurumin kotu ma ya yi tasiri.