1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dage zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Suleiman BabayoDecember 24, 2015

Firaminista Mahamat Kamoun ya bayyana cewar an makara wajen kai kayan aikin zaben kuma ana bukatar kara horos da wadanda za su yi aikin.

https://p.dw.com/p/1HTV2
Mahamat Kamoun
Hoto: PABANDJI/AFP/Getty Images

An dage zabukan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da aka tsara gudanarwa ranar Lahadi mai zuwa da tsawon kwanaki uku, har zuwa ranar 30 ga wannan wata na Disamba. Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin wucin gadi suka tabbatar da haka a wannan Alhamis.Firaminista Mahamat Kamoun ya ce an matsa da zaben saboda takardun kuri'u sun isa kasar a makare, sannan ma'aikata zaben suna bukatar samun karin horo.

An tsara zabukan na shugaban kasa da 'yan majalisa domin mayar da kasar bisa tafarkin demokaradiyya, bayan kifar da gwamnati da 'yan tawayen kungiyar Seleka ta galibi Musulmai suka yi cikin shekara ta 2013, abin da ya jefa kasar cikin rikici tsakanin Musulmai marasa rinjaye da kuma Kiristoci da suka fi yawa. Karkashin tsarin Shugabar gwamnatin wucin gadi Catherine Samba-Panza ba ta cikin 'yan takara. Akwai masu zabe kimanin milyan biyu. Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kimanin 11,000 suke aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.