An dage yanke hukunci kan tsige Murtala Nyako | Labarai | DW | 30.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage yanke hukunci kan tsige Murtala Nyako

Babbar kotun tarayya a Legas da ke Najeriya ta sanar da dage yanke hukunci kan sahihanci ko akasin haka na tsige Murtala Nyako daga kujerar gwamnan Adamawa.

Alkalin da ke jagorantar shari'ar Obon Abang ya ce ya dauki matakin na dake zartar da hukuncin bisa wani korafi da lauyan mai kare Gomna jihar da ke rikon kwarya Ahmadu Fintiri ya gabatar.

Mai shari'a Obon dai ya ce sai ranar 16 ga Oktoba mai zuwa ne kotu za sake zama da nudin sanar da hukuncin da ta yanke.

Ahmed Sajo da ke zaman mai magana da yawun tsohon gwamna Murtala Nyako ya shaidawa wakilin DW a Legas Masur Bala Bello cewar suna zargin sanya siyasa cikin wannan mataki da da kotun ta dauka.