1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dage ficewar Birtaniya daga EU zuwa 2020

Gazali Abdou Tasawa MNA
October 28, 2019

Lokacin da ya rage kwanaki uku wa'adin ficewar Birtaniya daga EU ya cika, Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da dage wa'adin har ya zuwa ranar 31 ga watan Janerun sabuwar shekara.

https://p.dw.com/p/3S4Sp
Großbritannien Brexit Symbolbild
Hoto: Getty Images/AFP/T. Akmen

Shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar ta EU, Donald Tusk ya sanar da wannan mataki a wani sako da ya wallafa a wannan Litinin a shafinsa na Twitter inda ya ce illahirin kasashen kungiyar ta EU 27 suka amince da matakin dage wa'adin na Brexit har ya zuwa 31 ga watan Janerun shekara ta 2020 a maimakon 31 ga wannan wata na Oktoba da yarjejeniyar baya ta tanada.

Sai dai kuma a karkashin sabon wa'adin wanda shi ne na uku tun bayan da al'ummar Birtaniya ta kada kuri'ar amincewa ta fita daga cikin kungiyar ta EU, Birtaniya na da damar ficewa daga cikin kungiyar ta EU tun a ranar 30 ga watan Nowamba ko kuma ranar 31 ga watan Disemba da ke tafe idan har aka yi wa yarjejejniyar gyaran fuska kafin cikar wa'adin ficewar.