An dage tattaunawa kan nukiliyar Iran | Labarai | DW | 20.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage tattaunawa kan nukiliyar Iran

A makon gobe ne idan Allah ya kaimu za koma kan teburin tattaunawa tsakanin Iran da kasashen nan shidda da ke shiga tsakani kan shirinta na nukiliya.

Mukaddashin minsitan harkokin wajen Iran din Abbas Araghch ya ce a halin yanzu ana bukatar tuntubar juna da yin shawarwari a bayan fage kafin komawa kan teburin tattauna a ranar Laraba mai zuwa ko da dai bai ambaci inda za a yi zaman ba.

Gabannin komawa zaman dai sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry zai je birnin London gobe don zantawa da takwarorinsa na Jamus da Faransa da ita kanta Burtaniya din don yin shawarwari.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Iran ke jan kunnen kasashen duniya musamman ma Amirka kan kauracewa yi wa Tehran matsin lamba muddin ana son cimma yarjejeniya kan batun. A karshen wannan watan da muke ciki ne dai wa'adin da aka diba don cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran din ke cika.