An cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Plateau | Siyasa | DW | 29.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Plateau

Al'ummar Berom da Fulani a wasu yankunan kananan hukumomin na arewacin jihar Plateau, sun cimma yarjejeniyar sulhu, a zaman mahawara da tattaunawar da ta gudana a Jos.

A ranar litinin da yammaci ne aka kai ga wannan yarjejeniya bayan wata tautaunawa ta zaman lafiya tsakanin wakilen gwamnatin jihar, jami'an tsaro tare da masu ruwa da tsaki kan sha'anin zaman lafiya a jihar .

Kafin a kai ga wannan matsayar, sai da jami'an tsaro a jihar Plateau suka yi ganawa a lokuta daban daban, tare da wakilen al'ummomin Berom da Fulani game da matakai da suka kamata a dauka don dakatar da hare hare, biye sace dabbobi da bangarorin biyu ke zargin juna. To bayan an tashi a taron Hardon Bacit dake Khr. Riyom Mohammed Bello Uthman, yace za'a sami nassarar wannan taralliya ce kawai idan anbi waddan nan ka'idojin daya zayyana

Wakilan Fulani da Berom daga yankunan Barkin Ladi, jos ta arewa, jos ta Kudu da Karamar hukumar Riyom ne suka hallara tare da jami'an tsaro kafin aka kai ga wannan yarjejeniya, inda kuma bayan wakilen kabilun biyu sun ammayar da abin dake ci musu tuwo a kwarya, abisani dai an kai ga wannan yajejeniya gaban wakilen gwamnatin Plateau, komshinan 'yan sanda tare da komandan rundunar STF, don haka nema shugaban karamar hukumar Riyom Sam Gyang Audu yace yana da yakinin samun masalaha a taron na yau.

Photograph made available 25 January 2010 shows a Nigerian women walking past soldiers patrolling in the Nigerian city of Jos following a week of religious violence in the central Plateau district, Nigeria 22 January 2010. Fighting between gangs of Christian and Muslim youths claimed more than 300 lives with millions of Naira worth of properties destroyed and hundreds of people displaced. EPA/GEORGE ESIRI

Sojoji a bakin aiki

Kafin wannan ganawa ta yau, a can bayan dukkanin kabilun biyu sun zargi jami'an tsaro na STF da lefin nuna son kai a bakin aiki, lamarin daya kai ga Fulani ke zargin dakarun STF da yin ko oho da kone-konen gidajen da Berom ke musu, kana su Berom ke zargin cewar sojoji ne ke kai musu hare hare cikin dare, to sai dai komandan rundunar ta STF major janar Henry Anyoola, ya ce aikin soja ba siyasa ba ce.

Yana cewar rundunar STF ba tana aiki na din din din bane, don haka bata nuna wa wani bangare goyon baya, tazacigabada aiki datake tare da nuna gaskiya ga kowa da kowa.

Yanzu dai jama'a sun zuba ido ne ganin ko wata kila tare da wannan mataki za'a shawo kan rigingimun tsakanin Fulani da Berom wanda aka shafe shekaru ana yi a wannan yanki na arewacin jihar Plateau.

( Ana iya sauraron sauti daga kasa)

Mawallafi: Abdullahi Maidawa Kurgwi
Edita : Zainab Mohammed Abubakar


Sauti da bidiyo akan labarin