An cimma yarjejeniyar sulhu a rikicin Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 23.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniyar sulhu a rikicin Sudan ta Kudu

Gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye sun rattaba hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta, duk da cewar har yanzu akwai ayar tambaya dangane da cimma nasarar aiwatar da ita.

Bayan gwabza fada na makonni biyar da yammancin wannan Alhamis din ce, gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da 'yan tawayen kasar suka rattabata hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wuta. Bangarorin biyu sun yi alkawarin tsagaita wuta nan da sao'i 24 masu gabatowa.

Cimma yarjejeniyar dai na nufin kawo karshen rikicin da ya haddasa mutuwar dubban mutane, tare da watsar da wasu dubu dari biyar, da barkewan rikicin a ranar 15 ga watan Disamban shekarar da ta gabata. A birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia ne dai shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar suka rattaba hannu a yarjejeniyar ta tsagaita wuta a bainar kungiyar IGAD mai shiga tsakani. Mai shiga tsakani a bangaren gwamnatin Sudan ta kudu Nhial Deng ya ce, duk da rattaba hannu da ak cimma a yau, da sauran rina a kaba dangane da aiwatar yarjejeniyar da ake saran zai kawo karshen wannan rikici.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu