An cimma yarjejeniya kan yaki da dumamar yanayi | Labarai | DW | 12.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniya kan yaki da dumamar yanayi

Wakillan kasashe 195 da ke halartar babban taro kan sauyin yanayi a Bourget kusa da birnin Paris, sun cimma yarjejeniya kan yaki da dumamar yanayi a rana ta 13 ta wannan taro.

Da misalin karfe bakoye da rabi ne dai agogon kasar Faransa Ministan harkokin wajan kasar ta Faransa Laurent Fabius, wanda shi ne shugaban wannan taro na COP21 kan dumamar yanayi, ya dau magana a gaban mahalarta taron inda ya ce:

" Ina kallon kowa da kowa da ke cikin wannan zaure, kuma na ji cewa dukanninku kun aminta da wannan yarjejeniya, domin ban ji wadanda suka nuna adawarsu da ita ba, don haka wannan yarjejeniya ta kasance amintatta."

Ga baki daya mahalarta taron na Bourget da ke Arewacin birnin Paris suka tabawa kalamman na Fabius abun da ke tabbatar da amincewa kowa da kowa. Tsawon kwanaki 13 ne dai taron ya dauka maimakon 12 kamar yadda aka tsara da farko.