1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniya kan kasafin kudin kungiyar EU na tsawon shekaru 7

Mohammad Nasiru AwalDecember 17, 2005

An kai ga wannan matsayi bayan da Birtaniya ta yarda a zaftare rangwamin da ake mata.

https://p.dw.com/p/Bu3J
Tony Blair a wajen taron kolin EU
Tony Blair a wajen taron kolin EUHoto: AP

Bayan tattaunawa da cece-kuce na tsawon kwanaki da sanyin safiyar yau asabar dukkan mahalarta taron kolin KTT a birnin Brussels sun amince da wata yarjejeniya akan kasafin kudin kungiyar na matsakaicin lokaci. An dai cimma wannan yarjejeniya ce bayan da FM Birtaniya Tony Blair wanda kasarsa ke rike da shugabancin kungiyar a yanzu ya yarda ya yi watsi da rangwamin euro miliyan dubu 10.5 daga shekara ta 2007 zuwa ta 2013. An fi mayar da hankali ne akan yawan kudin da za´a ware amma a karshe shugabannin tarayyar Turan sun amince da kasafin kudi na euro miliyan dubu 862 na tsawon shekaru 7 masu zuwa. An fi kai ruwa rana ne akan ragwamin kudaden gudummawa da kungiyar ta EU ke yiwa Birtaniya. Ko da yake za´a ci-gaba da yi mata rangwami amma a tsawon lokacin sabon kasafin kudin Birtaniya ba zata samu kimanin euro miliyan dubu 10.5 ba wato sama da miliyan dubu 2.5 kamar yadda Blair ya so da farko. A gare shi kam ba za´a yi cewa kwalliya ta mayar da kudin sabulu ba.

“Za´a ci-gaba da rangwamin in ban da a fannonin ba da taimakon bunkasa tattalin arzikin sabbin kasashen kungiyar EU. Ina ganin daidai ne kamar sauran kasashe mumu mu ba da ta mu gudummawa wajen fadada kungiyar.”

Wani batu da taron ya maar da hankali akai shi ne na rage yawan makudan kudaden tallafi ga manoma. Faransa wadda ta fi cin gajiyar wannan tallafi dai ita ce kan gaba wajen adawa da haka.

A cikin sanarwar bayan taro da suka bayar mahalarta taron sun amince su mikawa hukumar kungiyar EU rahoton farko a game da harkokin kashe kudin kungiyar a shekara ta 2008 ko ta 2009. Wannan rahoto zai hada har da na fannin aikin noma da kuma na rangwamin da ake yiwa Birtaniya. To sai dai ba sa ran yin wani gagarumin canji ga tallafin da ake ba manoma kafin wannan lokaci. A saboda haka shugaban Faransa Jaques Chirac ya nuna gamsuwa game da sakamakon taron musamman ganin yadda aka yiwa Faransa sassauci sakamakon hadin kan da take tsakaninta da Jamus.

“Tattaunawar ta nuna a fili cewa hadin kan dake tsakanin Jamus da Faransa yana aiki sosai. Hakan na da muhimmanci a garemu da kuma Turai baki daya.

Ga Jamus kuwa kara yawan kasafin kudin EU na matsayin wani kari ga gudummawar kudin da take ba kungiyar. To amma duk da haka yarjejeniyar kasafin kudin da aka cimma ba ta kai matsayin shawarar da kasar Luxemburg ta gabatar ba inji SGJ Angwela Merkel wadda ta bayyana sakamakon taron da cewa wata kyakkyawar mafita ce.

“Ina ganin yarjejeniyar da muka cimma hade da gudummawar da zamu bayar wani kyakkyawan sakamako ne da zamu iya gabatarwa ministan kudin mu gaba gadi.”

Baya ga kasafin kudin shugabannin Turan sun tabo batun kasar Iran, inda suka yi Allah wadai da sabuwar katobarar da shugaba Mahmud Ahmedi Nijad yayi inda ya nuna kyamar Isra´ila tare da karyata aukuwar kisan kiyashin da aka yiwa yahudawa a nahiyar Turai.