1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika shekara guda da mutuwar John garang

July 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuoZ

A kwana a tashi, yau shekara guda kenan, daidai da mutuwar tsofan mataimakin shugaban ƙasar Sudan, John Garang, bugu da ƙari tsohan madugun yan tawayen kudacin ƙasar, wanda ya rasa ran sa, cikin haɗarin jirgin sama.

Sanarwar daga fadar gwamnatin Khartum, ta ce nan gaba ko wace ranar 30 ga watan juli, zata zama ranar hutu, a faɗin Sudan baki ɗaya, domin nuna karamci da alhini, ga John Garang, mussaman ta la´akari, da kyaukyawar rawar da ya taka, wajen kwance ɗamara yaƙi, a kudancin Sudan.

Tsohuwar ƙungiyar tawayen SPLM, ta gudanar da addu´o´i da bisa jagoranci magadin mirganyin wato Salva Kiir, da kuma Rebekka Garang.

Kafafin sadarwa na Sudan, sun rubuta sharhuna iri iri, a game da wannan mutuwa.

Sakamakon binciken da aka gudanar kanta, ya haƙiƙance cewar mutuwa ce, ta Allah da Annabi, saɓanin yada wasu ke zato.

Saidai ya zuwa yanzu, da dama daga al´ummomin kudancin Sudan, bas u yarda da sakamakon binciken ba.