An ci gaba da barin wuta a Aleppo | Labarai | DW | 23.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ci gaba da barin wuta a Aleppo

Fada ya sake barkewa a Aleppo bayan da Rasha ta zargi 'yan tawaye da hana fararen fula ficewa daga birnin bayan tsagaita wuta

Ana yin mummunan barin wuta tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawaye a birnin Aleppo na kasar Siriya bayan karewar wa'adin tsagaita wutar da Rasha ta sanar Domin ba da damar kai wa fararen Hula tallafin jin Kai. Wannan dai na faruwa ne tun kafin majalisar Dinkin Duniya ta kwashe fararen hula daga yankunan da ke karkashin yan tawaye. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewaR an jiwo amon musayar wuta daga yankunan 'yan tawaye a gabashin kasar. Fararen hula fiye da 2000 aka jikata tun bayan kaddamar da farmakin domin kakkabe yan tawaye wadanda suka kame gundumomi a gabashin Siriyar tun shekarar 2012. Rasha ta zargi yan tawayen da hana fararen hula ficewa daga yankin.