An ceto ′yan cirani sama da 300 a Italiya | Labarai | DW | 29.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto 'yan cirani sama da 300 a Italiya

Mahukuntan Italiya sun ce a cikin sa'o'i 24 da suka gabata jami'ansu sun kubutar da 'yan cirani 379 da ke kokarin shiga kasar a kananan jiragen ruwa.

Gwamnatin Italiyan ta ce an ceto 41 daga cikin 'yan ciranin 'yan asalin tarayyar Najeriya da Ghana a kudancin Lampedusa, yayin da aka ceto 205 wanda ba a tantance kasashensu ba ya zuwa yanzu su ma dai a tsibirin na Lampedusa.

A daura da gabar ruwan Calabari ma hukumomin na Italiya sun ce sun ceci wasu 'yan Siriya da Eritrea su 133 wanda ke kokarin shiga kasar a cikin wani kankanin jirgin ruwa.

Tuni dai masu gadin gabar ruwan kasar ta Italiya suka ce sun mika 'yan ciranin da suka ceto zuwa wani sansani da ke Pozzallo a garin Sicily, inda nan ma 'yan ciranin ke yawan amfani da gabarsa wajen shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

Wata kididdiga da ma'aikatar cikin gidan Italiyan ta yi, ta nuna cewa kimanin kananan jiragen ruwa dauke da 'yan cirani sama da dubu 36 ne suka shiga kasar daga farko farkon wannan shekarar ya zuwa yanzu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh