An ceto wata mata da ranta a Nepal | Labarai | DW | 30.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto wata mata da ranta a Nepal

Kwanaki biyar bayan girgiza ƙasar da ta afka wa ƙasar an ceto wata matar cikin tarkaccen gine-ginen da suka ruguza.

Jami'an da ke yin aiki ceto na ƙasar Faransa a Nepal sun ce sun ceto wata matar da ranta a cikin tarkaccen gine-ginen da suka ruguje a Katmandu babban birnin ƙasar. Matar mai kimanin shekaru 30, jami'an sun ce tana cikin hayacinta ko da shi ke ma sun ce ta samu rauni.

Ta kuma shaida musu cewar tana cikin kicin tana yin girki a lokacin da ginin da take ciki ya ruguza da ita.Masu aikin ceton sun ce sun yi amfani da wata na'ura ta tanttance nufashi domin gano matar.