An ceto wasu baƙin haure a gaɓar tekun Libiya | Labarai | DW | 02.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto wasu baƙin haure a gaɓar tekun Libiya

Wani jirgin ruwa na soji na Faransa ya ceto baƙin haure 217 a gaɓar tekun Libiya.

Jirgin ruwan na gadin teku da Ƙungiyar Tarrayar Turai ta tura a tekun na Bahrum domin yaƙi da lamarin baƙin haure, ya ceto 'yan cirani kusan 217 a kusa da gaɓar tekun Libiya.

jami'an sun ce sun kame wasu mutane biyu matuƙa jirgin waɗanda suka ce za su miƙasu ga jam'ian tsaron Italiya.Yawanci fasinja da ke cikin jirgin 'yan ƙasashen Yankin Kudu da Hamada ne.