An ceto bakin haure a Teku | Labarai | DW | 28.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto bakin haure a Teku

Wani jirgin ruwan ceto dauke da bakin haure sama da 300 ya isa kasar Spain bayan tafiyar mako guda da ya yi a tekun Bahar Rum.

Jirgin ceton wanda mallakin wata kungiya ce ta Proactiva Open Arms, ya isa gabar ruwan Spain din ne a wannan Juma'a.

Galibin bakin hauren dai da aka ceto sun fito ne daga kasashen Somaliya da Najeriya da kuma kasar Mali.

A makon jiya ne aka ceto su a kusa da Libiya, sun kuma nufi Spain din ne bayan rashin samun sahalewar kasashen Malta da Italiya.

Hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da bakin haure dubu biyu da 200 suka mutu a kokarin da suke yi na ketara teku don shiga kasashen Turai a bana kadai.