An ceto baki da aka sace a Najeriya | Labarai | DW | 21.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto baki da aka sace a Najeriya

Rundunar jami'an 'yan sanda a Najeriya, ta ce an ceto wasu Amirkawa da wasu 'yan kasar Kanada da aka yi garkuwa da su a Kaduna a makon jiya.

Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram (Getty Images/AFP/Q. Leboucher)

'Yan sanda masu yaki da miyagun ayyuka a Najeriya

Su dai bakin da aka ceto, sun gamu da wadanda suka sace sun ne tsakanin garin Kafanchan da Kaduna a kan hanyarsu ta zuwa Abuja, a ranar Larabar da ta gabata. An dai kaiga rasa 'yan sanda biyu da ke rakiyar wadanda aka ceton.

'Yan sandan sun kuma ce suna tsare da wani mutum guda wanda ake zargi da sace mutanen, yayin kuma da ake ci gaba da aikin neman wasu da ke da hannu a lamarin. Can ma a yankin Niger Delta mai arzikin mai, bayanai sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu 'yan Najeriya da ke aikin hakar mai a yankin.