An cafke ′yan ci-rani 150 a arewacin Nijar | Labarai | DW | 02.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke 'yan ci-rani 150 a arewacin Nijar

Jandarmomin Jamhuriyar Nijar sun tsare mutanen ne a Arlit lokacin da suke kokarin ketara hamadar Sahara domin shiga kasar Aljeriya.

This photo taken on June 1, 2013, shows soldiers standing guard at the entrance of the main prison in Niamey. Inmates in Niamey's main prison killed two guards on June 1, officials said, a week after twin suicide bombings claimed 20 lives in the west African country. Three inmates charged with terrorist offences tried to had break out of the prison, prosecutor Ibrahim Wazir Moussa said on state television. AFP PHOTO / STRINGER (Photo credit should read STR/AFP/Getty Images)

Jami'an tsaron Nijar, a cikin aiki

A fadar hukumomin an cafke yan ci-ranin ne a ranakun Jumma'a da kuma jiya Asabar. Wata kafa ta tsaro ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, akasarin wadanda aka kama a hamadar Sahara maza ne da kuma yara kanana. Tuni ma dai aka tsare su a cibiyar jandarmomi da ke garin Arlit.

Da ma dai hukumomin Yamai sun sanar da cewa za su dau matakan ba sani ba sabo kan duk wadanda za a samu da hannu a kwasar 'yan ci-rani daga arewacin Nijar zuwa kasar Aljeriya ko kuma Libiya. Tuni ma dai suka sha alwashin rufe daukacin sansanonin 'yan ci-rani da ke arewacin kasar ta Nijar.Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne kwanaki kalilan, bayan da aka gano gawarwakin 'yan ci-rani da kishiruwa ya kashe a hamadar Sahara, a kokarinsu na zuwa Aljeriya domin inganta rayuwarsu.

A yanzu haka dai akwai 'yan ci-rani kimanin dubu biyar daga kasashe dabam-dabam na Afrika, da ke a wasu haramtattun sansanonin 'yan gudun hijira a Agadez da ke arewacin Nijar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman