An cafke wasu shugabannin Ƙungiyar Boko Haram | Labarai | DW | 30.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke wasu shugabannin Ƙungiyar Boko Haram

Hukumar leƙen asiri ta DSS a Najeriya ta sanar da cewar an kame wasu mutane waɗanda ake zargi da kasancewa 'Yan Boko Haram.

A cikin wata sanarwa da ta bayyana hukumar ta ce ta saka hannu a kan Usman shuai'bu wanda ake kira da sunan Money tare da wasu mutane tsakanin watan Yuli da Augusta a jihohin Legas da Kano da Plateau da Inugu da kuma Gombe.

Hukumar ta ce shuai'bun ya amince da cewar yana daga cikin shugabannin ƙungiyar wanda aka tura daga dajin sambisa domin kai hare-hare na ƙunar baƙin wake a cikin sassan ƙasar daban-daban.