An cafke shugaban yan adawa a Zimbabwe | Labarai | DW | 11.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke shugaban yan adawa a Zimbabwe

Yansanda a Zimbabwe sun cafke shugaban jamiiyyar adawa na wannan kasa,domin hana gudanar da zanga zanga na adduoi da yan adawan suka shirya gudanarwa.jamian yansandan sun cafke shugaban Jammiyar adawa ta MDC Morgan Tsvangirai da wasu manyan jammiansa na adawa ,bayan an tare hanyar da ayarin motocin da suke tafiya ciki kebi zuwa dandalin taro na birnin Harare,inda aka shirya gudanar da wannan Rallyin ayau.Wadanda suka ganewa idanunsu sun sanar dacewa jamian yansanda sunyi ta arangama da gangamin yan adawan ,wadanda sukayi da jifan su da duwatsu.Yanadawan dai na bukatar sauyi ne cikin harkokin siyasar kasar ta Zimbabwe,wadda ta jima akarkashin jagorancin shugaba Riobberta Mugabe da jammiyyarsa ta ZANU-PF tun da kasar ta samu yanci a 1980.