An cafke mutane da aka zarga da laifi a rubzawar gini a Bangladesh | Labarai | DW | 27.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke mutane da aka zarga da laifi a rubzawar gini a Bangladesh

Jami'an tsaro a ƙasar Bangaladesh sun shiga farautar masu hannu a sakacin da ya kai ga rugujewar ginin nan da ya rubta da ma'aikata.

Rescue workers look for trapped garment workers at the collapsed Rana Plaza building in Savar, 30 km (19 miles) outside Dhaka April 26, 2013. Bangladesh textile workers vented their anger on Friday, burning cars and clashing with police, as the death toll passed 312 following the collapse of a building housing factories that made low-cost garments for Western brands. Miraculously rescuers were still pulling people alive from the rubble - 72 since daybreak following 41 found in the same room overnight - two days after the eight-storey building collapsed on the outskirts of the capital, Dhaka. REUTERS/Andrew Biraj (BANGLADESH - Tags: DISASTER)

Ginin da ya ruguje a ƙasar Bangladesh

Kwanaki ukku bayan rubtawar gini mai hawa Takwas a Bangladesh, har yanzu ana ci gaba da zakulo mutanen da suka makale cikin buraguzen wannan gini.

Kawo yanzu fiye da mutane 300 suka rasa rayuka a hadarin,wannan ya gudana a daidai lokacin da ma'aikatan masaku daban-daban dake cikin ginin ke kan aiki.

A jiya Juma'a dubunan jama'a a Dakka babban birnin kasar, sun shirya zanga-zanga, domin cilastawa gwamnati ta cafke wanda suka mallaki gidan, da kuma shugabanin masana'antu da ke ciki.A yau jami'an tsaro sun bada labarin damko mutane biyu daga cikin su, a yayin da sauran suka shiga halin buya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman