An cafke dan gudun hijira a Jamus bisa yuwuwar kai hari | Labarai | DW | 21.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke dan gudun hijira a Jamus bisa yuwuwar kai hari

Mahukunta a Jamus sun ce akwai yuwuwar matashin dan gudun hijira daga Siriya yana da dangantaka da tsagerun IS da ke neman kai hare-hare kasashen Yammacin Duniya.

Mahukuntan Jamus sun bayyana cafke wani matashi dan shekaru 16 dan gudun hijira daga Siriya bisa yuwuwar dangantaka da tsagerun kungiyar IS masu neman kafa daular Islama. Mahukunta sun ce matashi barazana ne ga tsaro an cafke shi a birnin Cologne kamar yadda 'yan sanda da masu gabatar da kara suka tabbatar.

Jamus ta karfafa matakan tsaro sakamakon hare-hare da aka fuskanta masu nasaba da 'yan gudun hijira da ke neman mafaka, kuma kwararan dubban daruruwan 'yan gudun hijira a kasar ya kara nuna damuwa na yuwuwar samun hare-hare.