An bukaci zagaita wuta a zirin Gaza | Labarai | DW | 14.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci zagaita wuta a zirin Gaza

Biyo bayan artabun da aka kwashe sama da kwanaki hudu ana gwabza wa tsakanin Isra'ila da Hamas, Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a tsagaita wuta.

Babban sakataren  majalisar Antonio Guterres ya ce tashe-tashen hankullan ka iya ta'azzara matsalolin tsaro da rasa rayukka da kuma na agajin gaggawa, ba wai kawai a yankunan na Palasdinawa da Isra'ila ba har ma da wasu yankunan na daban.

Tuni dai aka fara samun zanga-zanga a wasu biranen kasashen duniya da suka hada da Jamus da Faransa da Labanon da dai sauransu. Shugaban Palasdinawan Mahmoud Abbas ya dora alhakin tsaida zubar da jinin da ake yi a Isra'ila da Gaza kan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.