1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Rasha na shan suka kan Navalny

Abdoulaye Mamane Amadou
September 3, 2020

Kasashe na ci gaba da yin matsin lamba a kan hukumomin Rasha da su fito su yi karin haske kan gubar da ake zargi sun sanya wa madugun adawa Alexei Navalny da ke kwance a wani asibiti a Jamus.

https://p.dw.com/p/3hvh2
Russland Moskau | Alexej Nawalny, Oppositionspolitiker
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Golovkin

Birtaniya ta bukaci Rasha ta fito fili ta bayyana gaskiyar lamarin, a yayin da ita kuma kungiyar EU ta yi wa batun kakkausar suka, daidai lokacin da a na ta bangare fadar gwamnatin Amirka White House ta bayyana cewa ta kadu da jin labarin, a yayin da Jamus ke shirin tattaunawa da kawayenta kan batun don cimma matsaya guda.

Binciken da aka gudanar a wani dakin gwaji na asibitin soja da ke Jamus, yayi nuni da cewa jagoran adawar na Rasha Navalny ya shaki wata guba ce mai sarke jijiyoyi, zargin da fadar gwamnatin Kremlin ta bayyana cewa za ta bayar da cikakken hadin kai wajen ci gaba da bincike, idan ta samu sakamakon farko na binciken da kwararru a fannin lafiyar suka yi a Jamus.